1 Kor 9:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata.

4. Ashe, ba mu da iko a ba mu ci da sha?

5. Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi?

6. Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai?

7. Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?

8. Wato, ina faɗar haka bisa ga ra'ayin mutum kawai ne? Ba haka ma Attaura ta faɗa ba?

1 Kor 9