13. Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka?
14. Haka nan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa, ya kamata masu sanar da bishara, a cishe su albarkacin bishara.
15. Amma ni kam, ban mori ko É—aya daga cikin halaliyan nan ba, ba kuma ina rubuta wannan ne, don a yi mini haka ba. Ai, gara in mutu a kan wani ya banzanta mini fahariyata.
16. Don ko da yake ina yin bishara, ba na fahariya da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona in ba na yin bishara!