1. Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji?
2. Ai, ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan manzo ba, lalle ku kam, ni manzo ne a gare ku, domin kuwa ku ne tabbatar manzancina a gaban Ubangiji.
3. Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata.
4. Ashe, ba mu da iko a ba mu ci da sha?
5. Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi?
6. Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai?