1 Kor 9:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji?

2. Ai, ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan manzo ba, lalle ku kam, ni manzo ne a gare ku, domin kuwa ku ne tabbatar manzancina a gaban Ubangiji.

3. Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata.

1 Kor 9