12. Haka ma yake a gare ku. Tun da yake kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikkilisiya.
13. Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yă yi addu'a a yi masa baiwar fassara.
14. In na yi addu'a da wani harshe, ruhuna ne yake addu'a, amma tunanina bai amfana kowa ba.
15. To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu'a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina.
16. In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba?
17. Ko da yake ka gode wa Allah sosai, ai, ɗan'uwanka bai ƙaru da kome ba.
18. Na gode Allah ina magana da waɗansu harsuna fiye da ku duka.
19. Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.
20. Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako.