19. Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.
20. Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
21. Domin a wajen cin abinci, kowa yakan dukufa a kan akushinsa, ga wani yana jin yunwa, ga wani kuwa ya sha ya bugu.
22. A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.
23. Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,
24. bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”
25. Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.”
26. Wato, duk sa'ad da kuke cin gurasar nan, kuke kuma sha a ƙoƙon nan, kuma ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.
27. Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a ƙoƙon nan na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa ke nan.
28. Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.
29. Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta wurin ci da sha da ya yi.
30. Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci.