Zak 5:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama.

2. Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.”

3. Sa'an nan ya ce mini, “Wannan la'ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya.

4. Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”

5. Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.”

Zak 5