Zak 12:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'an nan iyalan Yahuza za su ce wa kansu, ‘Ubangiji Allah Maɗaukaki yana ƙarfafa mutanensa waɗanda suke zaune a Urushalima.’

6. “A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al'umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.

7. “Ubangiji zai fara ba mutanen Yahuza nasara, domin kada darajar jama'ar Dawuda da ta mazaunan Urushalima ta fi ta mutanen Yahuza.

8. A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama'ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala'ikan Ubangiji a gabansu.

9. A ranar kuma zan hallaka dukan al'umman da suka zo su yi yaƙi da Urushalima.

10. “Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.

Zak 12