1. Ga maganar Ubangiji game da Isra'ila. Ubangiji wanda ya shimfiɗa sammai, ya kirkiro duniya, ya kuma sa rai a cikin mutum, ya ce,
2. “Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al'ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.