Zab 75:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka!Muna shelar sunanka mai girma,Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!

2. “Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah,“Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.

3. Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace,Zan ƙarfafa harsashin gininta.

4. Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama,Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,

5. Na dai faɗa musu su daina yanga,Su daina yin taƙama.”

6. Hukunci ba daga gabas, ko yamma,Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba.

7. Allah yake yin shari'a,Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.

8. Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo,Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi,Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha,Suka shanye shi ƙaƙaf.

Zab 75