8. Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9. Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10. Sarakunan Esbanya da na tsibirai,Za su ba shi kyautai,Sarakunan Arabiya da na HabashaZa su kawo masa kyautai.
11. Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa,Dukan sauran al'umma za su bauta masa!
12. Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi,Da waɗanda suke da bukata,Da waɗanda ba a kula da su.
13. Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.