Zab 59:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji,Ka mai da al'ummai duka abin bandariya!

9. Mai tsarona, kai ne kake kiyaye ni,Kai ne mafakata, ya Allah.

10. Allahna wanda yake ƙaunata, zai zo gare ni,Zai sa in ga an kori magabtana.

11. Kada ka kashe su, ya Allah, don kada jama'ata su manta.Ka watsar da su da ikonka, ka hallaka su ya Ubangiji mai kiyaye mu!

12. Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne,Da ma a kama su saboda girmankansu,Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!

Zab 59