Zab 59:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne,Da ma a kama su saboda girmankansu,Domin suna la'antarwa, suna ƙarya!

13. Da fushinka ka hallaka su,Ka hallaka su ɗungum.Sa'an nan jama'a za su sani Allah yana mulkin Isra'ila,Mulkinsa ya kai ko'ina a duniya!

14. Da maraice maƙiyana suka komo,Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.

15. Suna kai da kawowa ko'ina neman abinci,In ba su sami abin da ya ishe su ba,Sukan yi gunaguni.

16. Amma zan raira waƙa a kan ikonka,Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfiGa zancen madawwamiyar ƙaunarka.Kai mafaka ne a gare ni,Wurin ɓuya a kwanakin wahala.

17. Zan yabe ka, mai tsarona,Allah ne mafakata,Allah wanda ya ƙaunace ni.

Zab 59