1. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai,Gama na zo gare ka neman tsira.Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka,Sai dukan hatsari ya wuce.
2. Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki,Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3. Daga sammai Allah zai amsa mini,Zai kori waɗanda suka tasar mini,Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4. Raina yana tsakiyar zakoki,Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5. Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!