4. Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni,Ba wanda zai kiyaye ni,Ba kuwa wanda ya kula da ni.
5. Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako,Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni,Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.
6. Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako,Gama na nutsa cikin fid da zuciya.Ka cece ni daga maƙiyanaWaɗanda suka fi ƙarfina.
7. Ka cece ni daga cikin wahalata,Sa'an nan zan yabe ka cikin taron jama'arka,Domin ka yi mini alheri.