Yush 9:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu,Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!

12. Ko sun goyi 'ya'ya,Zan sa su mutu tun ba su balaga ba.Tasu ta ƙare sa'ad da na rabu da su!”

13. Ya Ubangiji, na ga yadda IfraimuTa mai da 'ya'yanta ganimaTana fitar da su zuwa wurin yanka.

14. Ya Ubangiji, me zan ce ka ba su?Me za ka ba su?Ka ba su cikin da ba ya haihuwa da busassun mama.

Yush 9