1. “Ku ji wannan, ya ku firistoci!Ku saurara, ya mutanen Isra'ila!Ku kasa kunne, ya gidan sarki!Gama za a yi muku hukunci,Domin kun zama tarko a Mizfa,Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.
2. Sun tayar, sun yi zurfi cikin zunubi,Zan hore su duka.
3. Na san Ifraimu, Isra'ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.Gama Ifraimu ta yi aikin karuwanci,Isra'ila kuma ta ƙazantu.
4. “Ayyukansu ba su bar suSu koma wurin Allahnsu ba,Gama halin karuwanci yana cikinsu,Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.