4. Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida.
5. Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.