Yush 3:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sai na ba da sadakinta a bakin tsabar azurfa goma sha biyar, da buhu biyu na sha'ir.

3. Sa'an nan na ce mata, “Ki keɓe kanki kwanaki da yawa domina, kada ki yi kwartanci, ki kwana da wani, ni kuma ba zan shiga wurinki ba.”

4. Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida.

5. Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.

Yush 3