1. Ifraimu tana kiwon iska,Tana ta bin iskar gabas dukan yini.Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya.Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya,Tana kai mai a Masar.”
2. Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza,Zai hukunta Isra'ila saboda hanyoyinta,Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.
3. A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa,Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.
4. Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye.Ya yi kuka, ya roƙi albarka.Ya sadu da Allah a Betel,A can Allah ya yi magana da shi.
5. Ubangiji Allah Mai Runduna,Sunansa Ubangiji,
6. Sai ku koma wurin Allahnku,Ku yi alheri, ku yi adalci,Ku saurari Allahnku kullayaumin.
7. Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma'aunin algus a hannunsa.Yana jin daɗin yin zalunci.
8. Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai,Mun samar wa kanmu dukiya.A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’
9. Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar,Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai,Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.
10. “Na yi magana da annabawa,Ni ne na ba da wahayi da yawa,Da misalai kuma ta wurin annabawa.