1. “A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi,Daga cikin Masar na kirawo ɗana.
2. Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini,Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi,Suna ƙona turare ga gumaka.
3. Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya.Na ɗauke su a hannuna,Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.
4. Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna,Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu.Na sunkuya, na ciyar da su.