Yow 1:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Abin da ɗango ya bari fara ta ci,Abin da fara ta bari burduduwa taci.

5. Ku farka, ku yi ta kuka, kubugaggu,Ku yi kuka, ku mashayan ruwaninabi,An lalatar da 'ya'yan inabinDa ake yin sabon ruwan inabi da su.

6. Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,Tana da ƙarfi, ba ta kumaƙidayuwa,Haƙoranta suna da kaifi kamar nazaki.

7. Ta lalatar da kurangar inabinmu,Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.Ta gaigaye ɓawo duka,Saboda haka rassan sun zama farifat.

8. Ya jama'a, ku yi kukaKamar yarinyar da take makokinrasuwar saurayinta.

Yow 1