Yah 4:30-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai suka fito daga garin suka nufo shi.

31. Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”

32. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”

33. Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?”

34. Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.

35. Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi.

36. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.

37. A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’

38. Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”

39. Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”

40. Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan.

41. Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa.

Yah 4