7. Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal.
8. Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai.
9. Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango,
10. ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”
11. Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12. Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.
13. Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.