Yah 13:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yesu ya ce masa, “Wanda ya yi wanka ba ya bukatar wanke kome, sai ƙafafunsa kawai, domin ya riga ya tsarkaka sarai. Ku ma tsarkakakku ne, amma ba dukanku ne ba.”

11. Don ya san wanda zai bāshe shi, shi ya sa ya ce, “Ba dukanku ne tsarkakakku ba.”

12. Bayan ya wanke ƙafafunsu, ya yafa mayafinsa, sai ya sāke kishingiɗa, ya ce musu, “Kun gane abin da na yi muku?

13. Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.

14. Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna.

15. Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku

16. Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi.

17. In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.

18. Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’

19. Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.

20. Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”

21. Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.”

22. Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake.

23. Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.

24. Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”

Yah 13