W. Yah 18:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan haka, na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa.

2. Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce,“Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi!Ta zama mazaunin aljannu,Matattarar kowane baƙin aljani,Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.

3. Dukkan al'ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

4. Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa,“Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata,Kada zunubanta su shafe ku,Kada bala'inta ya taɓa ku.

5. Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama,Allah kuwa ya tuna da laifofinta.

6. Ku saka mata daidai da yadda ta yi,Ku biya ta ninkin ayyukanta,Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.

7. Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci,Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka.Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake,Ni ba gwauruwa ba ce,Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’

8. Saboda haka, bala'inta zai aukar mata rana ɗaya,Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa.Za a kuma ƙone ta,Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”

9. Sarakunan duniya kuma da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunarta,

10. za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce,“Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni!Ya kai birni mai ƙarfi, Babila!A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”

11. Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙin ciki, tun da yake, ba mai ƙara sayen kayansu,

W. Yah 18