W. Yah 12:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta.

2. Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda.

3. Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.

4. Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.

5. Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al'ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.

6. Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.

7. Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika'ilu da mala'ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala'ikunsa suka yi ta yaƙi,

W. Yah 12