W. W. 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina kwance a gadona dukan dare,Ina mafarki da ƙaunataccena,Na neme shi, amma ban same shi ba.Na kira shi, amma ba amsa.

2. Bari in tashi yanzu in shiga birni,In bi titi-titi, in bi dandali-dandali,In nemi wanda raina yake ƙauna.Na neme shi, amma ban same shi ba.

3. Da matsaran da suke kai da kawowa cikin birni suka gan ni,Sai na tambaye su ko sun ga ƙaunataccena.

4. Rabuwata da matsaran ke nan,Sai na yi kaciɓis da ƙaunataccena.Na riƙe shi, ban sake shi ba,Na kai shi gidanmu, har ɗakin mahaifiyata.

5. Ku 'yan matan Urushalima,Ku rantse da bareyi da batsiyoyi,Ba za ka shiga tsakaninmu ba,Ku bar ta kurum.

W. W. 3