1. Ya 'yan'uwa, ko ba ku sani ba, shari'a tana da iko da mutum, muddin yana raye ne kawai? Da waɗanda suka san shari'a fa nake.
2. Misali, mace mai aure, shari'a ta ɗaure ta ga mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan.
3. Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.
4. Haka kuma 'yan'uwana, kun zama matattu ga Shari'a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah.
5. Ai, dā sa'ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha'awa wadda faɗakarwar Shari'a take sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa.
6. Amma a yanzu mun 'yantu daga Shari'a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka'idodi ba.
7. To, me kuma za mu ce? Shari'a zunubi ce? A'a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari'a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari'a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba.
8. Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari'a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri.
9. Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.