Neh 5:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai mata da maza suka yi ta kuka ƙwarai saboda 'yan'uwansu Yahudawa.

2. Akwai waɗanda suka ce, “Mu da 'ya'yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”

3. Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

Neh 5