36. “Za mu kuma kawo 'ya'yan farinmu maza, da na shanunmu, da na tumaki, da awaki, kamar dai yadda aka rubuta a dokoki, haka za mu kawo su a Haikalin Allahnmu, da gaban firistocin da suke hidima a Haikalin Allahnmu.
37. “Za mu kuma kawo hatsinmu na fari kullum, da sadakokinmu, da 'ya'yan itatuwanmu, da sabon ruwan inabi, da mai, a gaban firistoci, a shirayin Haikalin Allahnmu.“Za mu kuma ba Lawiyawa zakar amfanin gonakinmu, gama Lawiyawa ne suke tara zaka a garuruwanmu na karkara.
38. Firist kuwa daga zuriyar Haruna zai kasance tare da Lawiyawa sa'ad da suke karɓar zakar. Lawiyawa kuma za su fid da zaka daga cikin zakar da aka tara musu, su kawo ɗakin ajiya na Haikalin Allah.
39. Gama jama'ar Isra'ila da Lawiyawa za su kawo sadakoki na hatsi,da na ruwan inabi, da na mai, a ɗakin ajiya inda tasoshin Haikali suke, da gaban firistocin da suke hidima, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa.“Ba za mu ƙyale Haikalin Allahnmu ba.”