Mika 3:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ku ji wannan, ya ku shugabanninjama'ar Yakubu,Da ku sarakunan mutanen Isra'ila,Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya,Kuna karkatar da dukan gaskiya.

10. Kuna gina Sihiyona da jini,Kuna kuwa gina Urushalima dazalunci.

11. Shari'ar shugabannin ƙasar ta cinhanci ce.Firistocinta suna koyarwa donneman riba,Haka kuma annabawa suna annabcidon neman kuɗi.Duk da haka suna dogara gaUbangiji, suna cewa,“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,Ba masifar da za ta same mu.”

Mika 3