1. Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya kushugabannin mutanen Yakubu,Da ku sarakunan Isra'ila.Ya kamata ku san shari'a.
2. Amma kuna ƙin nagarta, kunaƙaunar mugunta,Kuna feɗe mutanena,Kuna kuma fizge naman jikinsu dagaƙasusuwansu.
3. Kuna cin naman mutanena, kunafeɗe fatar jikinsu,Kuna kakkarya ƙasusuwansu,Kuna yanyanka su gunduwagunduwa kamar naman da za a saa tukunya.”
4. Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji,Amma Ubangiji ba zai amsa musuba.Zai ɓoye musu fuskarsa a wannanlokaci,Saboda mugayen ayyukansu.
5. Ga abin da Ubangiji ya ce a kanannabawan da suka bi damutanensa a karkace,Waɗanda suke cewa, “Salama,”sa'ad da suke da abinci,Amma sukan kai yaƙin shahadaGa wanda bai ba su abin sawa a bakaba.