6. “Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.
7. Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”
8. Mika ya ce, “Saboda wannan zan yibaƙin ciki, in yi kuka,Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.Zan yi kuka kamar diloli,In yi baƙin ciki kamar jiminai.
9. Gama raunin Samariya, ba yawarkuwa,Gama ya kai Yahuza,Ya kuma kai ƙofar jama'ata aUrushalima.”
10. Kada a faɗe shi a Gat,Sam, kada a yi kuka.Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.
11. Ku mazaunan Shafir, ku wuceabinku da tsiraici da kunya.Mazaunan Za'anan ba su tsira ba.Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zaitumɓuke harasashin gininki.”