Mat 5:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna, almajiransa kuma suka zo gunsa.

2. Sai ya buɗe baki ya koya musu.

3. “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.

4. “Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.

Mat 5