17. Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice?
18. Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.
19. Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.
20. Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”
21. Yesu ya tashi daga nan, ya tafi zuwa ƙasar Taya da Sidon.
22. Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”
23. Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.”
24. Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”
25. Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”
26. Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”
27. Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”
28. Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.