1. A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci.
2. Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.”
3. Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?
4. Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?
5. Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa?
6. Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan.
7. Da kun san ma'anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba.
8. Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
9. Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu.