1. Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2. To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,
3. da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,
4. da Saminu Bakan'ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
5. Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.
6. Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila,Irm
7. kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’
8. Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.
9. Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,