1. “Yanzu firistoci, ga umarni dominku.
2. Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
3. Ga shi, zan tsauta wa 'ya 'yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa'an nan zan kore ku daga gabana.
4. Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
5. “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.
6. Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.