M. Sh 9:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Bayan dare arba'in da yini arba'in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, wato alluna na alkawarin.

12. “Sa'an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’

13. “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘Na ga mutanen nan suna da taurinkai.

14. Bari in hallaka su, in shafe sunansu daga duniya, sa'an nan in maishe ka wata al'umma wadda ta fi su iko da kuma yawa.’

15. “Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta.

16. Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi.

17. Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku.

18. Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.

19. Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci.

M. Sh 9