M. Sh 6:14-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Kada ku bi waɗansu alloli na al'umman da suke kewaye da ku,

15. gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.

16. “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.

17. Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su.

18. Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

19. Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.

20. “Idan nan gaba 'ya'yanku suka tambaye ku ma'anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su,

21. sai ku amsa wa 'ya'yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir'auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko.

22. A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu'ujizai gāba da Masarawa, da Fir'auna, da dukan gidansa.

23. Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu.

24. Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau.

25. Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.’ ”

M. Sh 6