M. Sh 4:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Shi ne ya hurta muku shari'ar da ya umarce ku ku kiyaye, wato dokokin nan goma. Ya rubuta su a allunan dutse guda biyu.

14. Duk da haka Ubangiji ya umarce ni in koya muku dokokin da farillan don ku aikata su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta.”

15. “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.

16. don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,

17. ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama,

18. ko siffar kowane abu mai jan ciki bisa ƙasa, ko siffar kifin da yake cikin ruwa ƙarƙashin ƙasa.

19. Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.

20. Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.

M. Sh 4