19. Amma matanku, da 'ya'yanku, da dabbobinku, na sani kuna da dabbobi da yawa, su ne za ku bari a garuruwan da na ba ku,
20. har lokacin da Ubangiji ya zaunar da 'yan'uwanku kamar yadda ya zamshe ku, su ma su mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba su a hayin Urdun, sa'an nan kowa zai koma ga mallakarsa.’
21. “A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.
22. Kada kuwa ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku ne zai yi yaƙi dominku.’ ”
23. “Sa'an nan kuma na roƙi Ubangiji, na ce,
24. ‘Ya Ubangiji Allah, kai ne ka fara nuna wa baranka ɗaukakarka da ikonka. Ba wani Allah a Sama ko a duniya da zai aikata ayyuka na banmamaki irin naka.
25. Ka yarje mini, ina roƙonka in haye in ga wannan kyakkyawar ƙasa a hayin Urdun, ƙasan nan mai kyau ta tuddai, da Lebanon.’