M. Sh 29:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba.

6. Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku.

7. Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.

8. Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.

9. Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.

10. “Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila,

11. da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa.

12. Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau.

13. Don ya mai da ku jama'arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

14. Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba,

15. amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.

16. “Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al'ummai muka wuce.

17. Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya.

18. Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci.

M. Sh 29