M. Sh 29:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗannan ne zantuttukan alkawari da Ubangiji ya umarci Musa ya faɗa wa Isra'ilawa a ƙasar Mowab, wato banda alkawarin da ya yi da su a bisa Dutsen Horeb.

2. Sai Musa ya kira dukan Isra'ilawa ya ce musu, “Ai, kun ga dukan abin da Ubangiji ya yi wa Fir'auna da barorinsa a dukan ƙasar Masar.

3. Idanunku sun ga manyan wahalai, da alamu, da mu'ujizai masu girma.

4. Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.

5. Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba.

6. Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku.

7. Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.

8. Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.

9. Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.

M. Sh 29