4. Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.
5. Can za ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a taɓa sassaƙa su da baƙin ƙarfe ba.
6. Sai ku gina wa Ubangiji Allahnku bagade da duwatsun da ba a sassaƙa ba. A bisa wannan bagade za ku miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku.
7. Za ku kuma miƙa hadayu na salama ku ci a wurin, ku yi ta murna a gaban Ubangiji Allahnku.
8. Sai ku rubuta dukan kalmomin waɗannan dokoki su fita sosai bisa duwatsun nan.”