16. “Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.
17. “Kada ku karkatar da shari'ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina.
18. Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan.
19. “Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku.
20. Sa'ad da kuka kakkaɓe 'ya'yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
21. Sa'ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
22. Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”