7. Ko akwai wani mutum wanda yake tashin yarinya, amma bai aure ta ba tukuna? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani ya aure ta.’
8. “Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.’
9. Sa'ad da shugabannin yaƙi suka daina yi wa jama'a jawabi, sai a zaɓi jarumawan sojoji don su shugabanci mutane.
10. “Sa'ad da kuka kusaci gari don ku yi yaƙi, sai ku fara neman garin da salama.
11. In ya yarda da salamar, har ya buɗe muku ƙofofinsa, sai dukan mutanen da suke cikinsa su yi muku aikin gandu, su bauta muku.
12. Amma idan ya ƙi yin salama da ku, amma ya yi yaƙi da ku, sai ku kewaye shi da yaƙi.
13. Idan Ubangiji Allahnku ya bashe shi a hannunku, sai ku karkashe dukan mazaje da takobi.
14. Amma mata, da yara, da dabbobi, da dukan abin da yake cikin garin, da dukan ganimarsa, sai ku kwashe su ganima, ku mori ganimar magabtanku, wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
15. Haka za ku yi da dukan garuruwan da suke nesa da ku, wato garuruwan da ba na al'umman da suke kusa da ku ba.