6. “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra'ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa.
7. Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran 'yan'uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can.
8. Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”
9. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku shiga kwaikwayon ayyuka na banƙyama na waɗannan al'ummai.
10. Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa 'yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri,
11. ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha'ani da matattu.
12. Ubangiji yana ƙyamar mai yin waɗannan abubuwa. Saboda waɗannan ayyuka masu banƙyama shi ya sa Ubangiji Allahnku yake korar waɗannan al'ummai a gabanku.
13. Sai ku zama marasa aibu a gaban Ubangiji Allahnku.
14. “Gama waɗannan al'ummai da za ku kora suna kasa kunne ga masu maita da masu duba, amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.