1. “Lawiyawa da firistoci, wato dukan kabilar Lawi, ba su da rabo ko gādo tare da mutanen Isra'ila. Hadayun Ubangiji da dukan abin da ake kawo masa, su ne za su zama abincinsu.
2. Ba za su sami gādo tare da 'yan'uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu.
3. “To, ga rabon da jama'a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin.
4. Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.
5. Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da 'ya'yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.
6. “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra'ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa.